image image | transcript string | source string |
|---|---|---|
Waƙar Infiraji Ta Farko | 1 | |
Waƙar Majidu | 1 | |
Bismi l-Lāh al-Raḥmān al-Raḥīm | 1 | |
Wa ṣalla l-Lāhu ʿalā l-Nabiyyi l-Karīmi | 1 | |
Wa ʿalā ālihī wa ṣaḥbih wa sallam | 1 | |
Bismil l-Lāhi Majīdi | 1 | |
Na yi nufin waƙa jadīdī | 1 | |
In yabon manzo ḥamīdī | 1 | |
Dhu shafā Yawmal Miʿādi | 1 | |
Mai sonsa ba zai baƙin ciki ba | 1 | |
Rabbanā ya daɗin aminci | 1 | |
Gun mafificin mutunci | 1 | |
Ɗa wani nasa ɗan karumci | 1 | |
Wanda ka ba shugabanci | 1 | |
Ya yi horo ba da kangara ba | 1 | |
Rabbi na nufi wagga waƙa | 1 | |
Ta yabo nasa ba nifāqā | 1 | |
Taimake ni ka ban ḥadhāqā | 1 | |
In yi waƙa mai zalāqā | 1 | |
Ta yabo nasa ba da kuskure ba | 1 | |
Rabbanā ka yi min ijābā | 1 | |
In ga nai sallah a Ɗaiba | 1 | |
Har in tada ido in duba | 1 | |
In ga Koran nan ta gubba | 1 | |
In yi murna ba da fariya ba | 1 | |
Ya Ilāha l-ʿālamina | 1 | |
Taimakan ni in je Madina | 1 | |
In ji daɗi in yi murna | 1 | |
In ga qabrin ɗan Amina | 1 | |
Baban Kulthumu ɗan Suwaiba | 1 | |
A dare ka yi min ishārā | 1 | |
In ga na je nai ziyara | 1 | |
Gun kushewan na da nura | 1 | |
Ta cika shi na mai bushara | 1 | |
Ga Musulmi ba da kangara ba | 1 | |
Ka ji mai waƙar hululu | 1 | |
Tūba zanka yabon Rasulu | 1 | |
Musɗafa jikankKhalīlu | 1 | |
Gobe ka sha salsabīlu | 1 | |
Wanda ya fi ruwan zuma a gumba | 1 | |
Don mutum ne shi karimi | 1 | |
Mai yawan haƙuri ḥalīmi | 1 | |
Ya abokina ʿAsīmi | 1 | |
In ka so ka zame salami | 1 | |
Ya bi Annabi ba da sunkuye ba | 1 | |
Kafirai da sun fahimta | 1 | |
Bin Muhammadu ya kamata | 1 | |
Ambato nasa ya gabata | 1 | |
Can ga Attaura, ku huta | 1 | |
Ku bi Annabi ba da gardama ba | 1 | |
Ya kamata mu gode Allah | 1 | |
Can gabanmu akwai qabīla | 1 | |
An kashe su cikin jahālā | 1 | |
Mu zuwansa tazan fitilla | 1 | |
A gare mu ba mu yi zaman duhu ba | 1 | |
Shekarar ƙarnin dashensa | 1 | |
Ya katarta da maʼu nisa | 1 | |
Shi muke cin arzikinsa | 1 | |
Ka ga ba don shi ba da sa- | 1 | |
Muwa ba ta riski mai rashi ba | 1 | |
A’a in ba ka mayyaze ba | 1 | |
Gaskiya ba ta sa fita ba | 1 | |
Sai da ya zaka nuna turba | 1 | |
Ko duhu bai wartsake ba | 1 | |
Ba dan aiko shi duniya ba | 1 | |
Ɗan Amina muna yabonka | 1 | |
Don mafificin rabonka | 1 | |
Nai duʿaāʿi in gane ka | 1 | |
Zuciyata ba ta harka | 1 | |
In ban yi yabonka na natsa ba | 1 | |
Sanda an aiko shi shirya | 1 | |
Gaskiya ta kori ƙarya | 1 | |
Masu aikin ratse hanya | 1 | |
Ƙi da so wasu sun biyayya | 1 | |
Tamkar ba su gaji kangara ba | 1 | |
Shi mutum ne mai laɗafa | 1 | |
Kyan jiki da hali da siffa | 1 | |
Na ga Annabi ba khilāfā | 1 | |
Ko a baiwa ya fi sarfa | 1 | |
Ba shi kan kyauta shina bari ba | 1 | |
Ba shi rowa don ƙiyayya | 1 | |
An yi sammu gami da cinya | 1 | |
Aka ba shi a kan hamayya | 1 | |
Don yawan ladabi da kunya | 1 | |
Ya ci ba bisa kan rashin sani ba | 1 | |
Hankalinsa yana ga Allah | 1 | |
Bai kula ba, maras kasala | 1 | |
Gun yawan azumi da salla | 1 | |
Taimakonsa yana ga Allah | 1 | |
Ya ko isa jalla bai gaza ba | 1 | |
Rabbanā ya baza wanjin | 1 | |
Masu ƙinsa sabo da ƙwanjin | 1 | |
Arzikinsa ya haske ƙirjin | 1 | |
Annabinsa aboka bar jin | 1 | |
Maganarsu ba su yi muwāfaqā ba | 1 | |
Shi ya ɗaukaka ɓirbishinsu | 1 | |
Hassadarsu ta hallaka su | 1 | |
Aka karkashe galibinsu | 1 | |
Galibin wasu masu mussu | 1 | |
Suka tuba da sake ba shi gaba | 1 |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.