audio audioduration (s) 1.02 29.2 | text stringlengths 9 479 | speaker_id int64 2 1.88k |
|---|---|---|
An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji. | 1,880 | |
Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki. | 1,880 | |
Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah. | 1,880 | |
Waɗannan su ne manyan Edom. | 1,880 | |
Saura sun haɗa kai da Dawuda a Hebron Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa. | 1,880 | |
Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. | 1,880 | |
An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne. | 1,880 | |
Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji, ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. | 1,880 | |
Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. | 1,880 | |
Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu. | 1,880 | |
Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? | 1,880 | |
Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. | 1,880 | |
Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. | 1,880 | |
Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai. | 1,880 | |
Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku. | 1,880 | |
’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. | 1,880 | |
Zuriyar Shawulu mutumin Benyamin Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku, Noha na huɗu da Rafa na biyar. | 1,880 | |
Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. | 1,880 | |
Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. | 1,880 | |
Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. | 1,880 | |
Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya. | 1,880 | |
Akwai mutane dubu ashirin da hudu a sashensa. | 1,880 | |
Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi, Mika, Reyahiya, Ba’al, da Beyera, wanda Tiglat Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. | 1,880 | |
Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta. | 1,880 | |
Haran shi ne mahaifin Gazez. | 1,880 | |
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. | 1,880 | |
Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed Edom, da farin ciki. | 1,880 | |
Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin. | 1,880 | |
Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli, ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. | 1,880 | |
daya Tarihi Sura hudu | 1,880 | |
Eshton shi ne mahaifin Bet Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. | 1,880 | |
Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa. | 1,880 | |
daya Tarihi Sura shida | 1,880 | |
Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu. | 1,880 | |
Sai Dawuda ya kusato, sa’ad da Ornan ya duba sai ya gan shi, ya bar masussukar ya rusuna a gaban Dawuda da fuskarsa har ƙasa. | 1,880 | |
Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani. | 1,880 | |
’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni. | 1,880 | |
Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa. | 1,880 | |
daya Tarihi Sura ashirin | 1,880 | |
Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana. | 1,880 | |
Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa. | 1,880 | |
Zuriyar Lawi ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari. | 1,880 | |
’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. | 1,880 | |
Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi. | 1,880 | |
Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji. | 1,880 | |
Yebusiyawan da suke zama a wurin suka ce wa Dawuda, Ba za ka shiga nan ba. | 1,880 | |
Duka duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai | 1,880 | |
Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka. | 1,880 | |
Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji. | 1,880 | |
Aka ba zuriyar Merari, gida gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun. | 1,880 | |
Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. | 1,880 | |
Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. | 1,880 | |
Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima. | 1,880 | |
A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can. | 1,880 | |
Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu. | 1,880 | |
Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu, sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. | 1,880 | |
Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari. | 1,880 | |
Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. | 1,880 | |
Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi. | 1,880 | |
Ubangiji ya amsa masa ya ce, Ka tafi, zan ba da su gare ka. | 1,880 | |
Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar. | 1,880 | |
Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana. | 1,880 | |
Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. | 1,880 | |
Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila. | 1,880 | |
Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni. | 1,880 | |
Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa. | 1,880 | |
’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af. | 1,880 | |
Dawuda ya ce, Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla filla. | 1,880 | |
Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. | 1,880 | |
Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa. | 1,880 | |
Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’ | 1,880 | |
Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa. | 1,880 | |
Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist. | 1,880 | |
Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada. | 1,880 | |
Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. | 1,880 | |
Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe bushe da na kaɗe kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. | 1,880 | |
Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba. | 1,880 | |
Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu. | 1,880 | |
Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. | 1,880 | |
An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara. | 1,880 | |
daya Tarihi Sura goma sha shida | 1,880 | |
Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse. | 1,880 | |
Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba. | 1,880 | |
Na’aman, da Ahiya, da Gera. | 1,880 | |
To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. | 1,880 | |
Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya. | 1,880 | |
Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta. | 1,880 | |
Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya. | 1,880 | |
Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba. | 1,880 | |
’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram. | 1,880 | |
Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi. | 1,880 | |
Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne. | 1,880 | |
Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa. | 1,880 | |
Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel. | 1,880 | |
Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. | 1,880 | |
Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben Zohet. | 1,880 | |
Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada. | 1,880 | |
daya Tarihi Sura goma | 1,880 | |
Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda, Tafi ka faɗa wa Dawuda, Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku. | 1,880 | |
Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. | 1,880 |