Dataset Viewer
Auto-converted to Parquet Duplicate
audio
audioduration (s)
1.02
29.2
text
stringlengths
9
479
speaker_id
int64
2
1.88k
An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji.
1,880
Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.
1,880
Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
1,880
Waɗannan su ne manyan Edom.
1,880
Saura sun haɗa kai da Dawuda a Hebron Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.
1,880
Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi.
1,880
An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne.
1,880
Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji, ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.
1,880
Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila.
1,880
Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu.
1,880
Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka?
1,880
Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma.
1,880
Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda.
1,880
Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai.
1,880
Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku.
1,880
’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
1,880
Zuriyar Shawulu mutumin Benyamin Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku, Noha na huɗu da Rafa na biyar.
1,880
Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi.
1,880
Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist.
1,880
Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba.
1,880
Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.
1,880
Akwai mutane dubu ashirin da hudu a sashensa.
1,880
Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi, Mika, Reyahiya, Ba’al, da Beyera, wanda Tiglat Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta.
1,880
Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.
1,880
Haran shi ne mahaifin Gazez.
1,880
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
1,880
Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed Edom, da farin ciki.
1,880
Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin.
1,880
Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli, ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel.
1,880
daya Tarihi Sura hudu
1,880
Eshton shi ne mahaifin Bet Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash.
1,880
Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa.
1,880
daya Tarihi Sura shida
1,880
Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu.
1,880
Sai Dawuda ya kusato, sa’ad da Ornan ya duba sai ya gan shi, ya bar masussukar ya rusuna a gaban Dawuda da fuskarsa har ƙasa.
1,880
Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.
1,880
’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni.
1,880
Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa.
1,880
daya Tarihi Sura ashirin
1,880
Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana.
1,880
Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.
1,880
Zuriyar Lawi ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
1,880
’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza.
1,880
Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.
1,880
Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.
1,880
Yebusiyawan da suke zama a wurin suka ce wa Dawuda, Ba za ka shiga nan ba.
1,880
Duka duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai
1,880
Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.
1,880
Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.
1,880
Aka ba zuriyar Merari, gida gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
1,880
Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani.
1,880
Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda.
1,880
Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima.
1,880
A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can.
1,880
Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
1,880
Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu, sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh.
1,880
Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.
1,880
Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
1,880
Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.
1,880
Ubangiji ya amsa masa ya ce, Ka tafi, zan ba da su gare ka.
1,880
Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
1,880
Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
1,880
Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah.
1,880
Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila.
1,880
Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.
1,880
Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa.
1,880
’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af.
1,880
Dawuda ya ce, Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla filla.
1,880
Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni.
1,880
Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa.
1,880
Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’
1,880
Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa.
1,880
Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist.
1,880
Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada.
1,880
Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma.
1,880
Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe bushe da na kaɗe kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki.
1,880
Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.
1,880
Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu.
1,880
Na mutanen Zera su ne, Yewuyel.
1,880
An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara.
1,880
daya Tarihi Sura goma sha shida
1,880
Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse.
1,880
Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.
1,880
Na’aman, da Ahiya, da Gera.
1,880
To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa.
1,880
Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya.
1,880
Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.
1,880
Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.
1,880
Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.
1,880
’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram.
1,880
Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi.
1,880
Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne.
1,880
Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.
1,880
Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.
1,880
Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin.
1,880
Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben Zohet.
1,880
Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
1,880
daya Tarihi Sura goma
1,880
Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda, Tafi ka faɗa wa Dawuda, Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku.
1,880
Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan.
1,880
End of preview. Expand in Data Studio

Cleaned Hausa Speech Dataset v3

A cleaned and processed Hausa speech dataset built from multiple open-source Hugging Face datasets.

Dataset Description

This dataset contains cleaned, normalized, and deduplicated Hausa speech audio with aligned transcriptions. All audio is:

  • Sample rate: 16,000 Hz (mono)
  • Format: FLAC (lossless, embedded in Parquet)
  • Duration range: 1–30 seconds per clip
  • Loudness normalized: -20 dBFS RMS
  • VAD trimmed: Non-speech segments removed with crossfaded joins
  • Silence trimmed: Leading/trailing silence removed (25 dB threshold)
  • Deduplicated: By audio content hash and (text, speaker_id) pairs

Sources

Source Description
google/WaxalNLP Hausa TTS data from WaxalNLP
naijavoices/naijavoices-dataset NaijaVoices Hausa batches (0, 1, 2)
vpetukhov/bible_tts_hausa Bible TTS Hausa (single speaker)

Dataset Structure

Features

  • audio: Audio waveform (FLAC, 16kHz mono)
  • text: Hausa transcription (NFC-normalized Unicode)
  • speaker_id: Integer speaker identifier (unique per source × speaker)

Usage

from datasets import load_dataset

dataset = load_dataset("suleiman2003/W_hausa_v3", split="train")

# Play first sample
print(dataset[0]["text"])
print(dataset[0]["audio"]["sampling_rate"])  # 16000

Processing Pipeline

  1. Source Parquet files downloaded from HuggingFace Hub
  2. Audio decoded, resampled to 16kHz mono
  3. Silence trimming (25 dB threshold)
  4. WebRTC VAD trimming (aggressiveness=2) with 10ms crossfade
  5. RMS loudness normalization to -20 dBFS
  6. Quality filters: duration (1-30s), clipping ratio (<1%)
  7. Deduplication by audio hash and (text, speaker_id)
  8. FLAC encoding and Parquet sharding
Downloads last month
120