audio audioduration (s) 1.02 17.8 | text stringlengths 34 1.14k | speaker_id stringclasses 35
values | age_group stringclasses 5
values | domain stringclasses 1
value | gender stringclasses 2
values |
|---|---|---|---|---|---|
Rashin tanadi na iya jefa mutum cikin wahala idan wata lalurar gaugawa ta taso. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Idan mutum yana son guje wa matsalar rashin kuɗi, dole ne ya fara tanadi tun da wuri. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ado ya sayi tattasai da yawa ya shanya don nan gaba zai yi tsada | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Maimuna za ta sayi sabon famfo bayan tsohon ya fashe kwatsam. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ya ce saboda littattafan suna ƙara tsada idan an koma makarantu, shi ya sa yake saya cikin hutu | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Mun yanke shawarar shirya wasanni a gida domin jin daɗin hutunmu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yin tanadi domin gaugawa yana hana yawan damuwa da rashin kwanciyar hankali. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
An ware waɗanda za su share ɗakin taron bayan kammala bikin. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Idan mutum yana da hanyar samun kuɗi, yana da kyau ya ware wani kaso don ajiyar gaggawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yana da kyau mutum ya ware kaso na albashinsa don abubuwan da ba a zata ba. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Bukukuwa suna zama lokaci mai kyau na sadar da zumunci a tsakanin mutane. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ya kamata a rinƙa ware wani kaso na albashi domin ajiyewa saboda abin zai iya tasowa ba zato ba tsammani. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
An shirya gagarumin hawan daba, saboda naɗin sarautar sabon Yarima. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Tun watan maulidi na sayi dabbar da zan yanka da sallah don kar su ƙara tsada | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Babu wanda ya san abin da zai faru gaba, ya kamata mutum ya yi tanadi na gaugawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Nasir ya kawo wa Nadiya kajin maulidi da kuma toshi | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ba na so su tashi haka nan su tafi ba tare da na sani ba. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Sabiru ya shirya ajiyar kuɗi don sayen sabuwar waya idan tasa ta lalace. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Za mu tafi ƙauyenmu bayan an yi mana hutun makaranta | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Muna fatan yin bikin cikar shekara a wani wurin da babu hayaniya. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na tsara raba lokacin hutuna tsakanin iyali da abokai don kowa ya ji daɗi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
In sun dawo, wannan zai sa su koma makaranta a kan lokaci. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ya kamata mutum ya guji kashe kuɗi marar amfani don magance matsalolin gaggawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Khadija ta yanke shawarar siyan tirela ta ruwa daga Kaduna Water Board don magance matsalar ruwan famfo. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yana da kyau a samu wani asusun banki na musamman don ajiyar gaggawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
An sanya fitulu a ko'ina don ƙarawa bikin zagayowar shekarar armashi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Duk wani mai hankali yana tanadi don gujewa ruɗani a lokacin larura. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wata rana na samu matsala da mota, amma kudin da na tanada ya taimaka. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Mun haɗa kai domin yin ado na musamman don bikin hutun shekara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yin taron biki yana ba da damar ƙulla sabon zumunci. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Bello yana tara kudi a Jaiz Bank don gidansa zai iya buƙatar gyara a kowane lokaci. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Manyan gidanmu sun yanke shawarar wannan Kirsimetin za'a yi a gidan babbar yayarmu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ajiye kayan abinci da domin gujewa lokacin tsada abu ne mai kyau. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
A wasu gidaje, ana shirya gasar girki a lokacin bukukuwa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
A shekarar da ta gabata, Maimuna ta sayi sabuwar mota bayan tsohuwar tata ta lalace. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na fara tsara jerin abubuwan da za mu yi a lokacin hutun shekara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Idan kuwa aka tsara komai yadda ya dace, to sai a yi komai cikin nasara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Mun yi shawarar gudanar da liyafar cin abinci don murnar nasarorin da muka samu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
An shirya bikin karrama matashin da ya tsinci maƙudan kuɗaɗe ya mayar da su. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na lura cewa mutanen da ke da shiri na gaggawa sukan fi samun sauƙin rayuwa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Sadiya ta dage ta sayi komai tun cikinta yana ƙarami, saboda kar su ƙara tsada | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Samun inshorar lafiya ko motoci yana rage nauyin kashe kuɗi a lokaci mai tsanani. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na lura cewa ajiyar kuɗi yana taimakawa wajen guje wa shan wahala a lokacin matsala. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Lokacin da motata ta lalace, sai na ji daɗin cewa na riga na tanadi kuɗin gyara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Samun asusun ajiya na gaugawa yana taimakawa wajen magance matsalolin iyali ko karatu ko rashin lafiya. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Nasir ya sayi takalma don ya san za su ƙara tsada a gaba | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Safara’u ta tsara wasannin da yara za su yi lokacin hutun makaranta. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yana da kyau a tanadi abinci na musamman don bukukuwa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wata mata a Unguwar Kofar Mata tana ajiye dala domin bukatu na gaggawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na shirya tsaf don gudanar da gagarumin taro na haɗuwa da tsofaffin abokai. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
A bana, muna shirin yin sabuwar hanya ta gudanar da bikin cika shekarun haihuwa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Lokacin da ake shirin hutun bukukuwa, yana da kyau a shirya abinci da wasanni na nishaɗi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Mun tsara jerin abinci na musamman da za mu shirya domin liyafa a lokacin hutu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wataƙila Salisu zai jagoranci shirya liyafar barka da shigowar sabuwar shekara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na fahimci cewa yana da kyau mutum ya sami kuɗin tanadi na akalla wata uku. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ba a fasa ba, kawai dai ƙarancin lokacin nake kallo. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wasu mutane ba sa tunanin samun inshora, amma tana iya rage yawan kuɗin buƙatar gaugawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ka koyar da yara yadda za su tattala abubuwan amfani domin rage kashe kuɗi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ina nan ina shirin kai ku gidan makama ku yi kallo | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Sabiru ya fara ajiye kuɗi don guje wa wahala idan farashi ya ƙaru. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wasu iyalai suna amfani da bukukuwa domin tunawa da kakanni. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
A gidana muna tsara kyautuka tun kafin lokacin Kirsimeti yazo. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yana da kyau mutum ya ware kuɗi domin gyaran gida, matsala na iya tasowa kowane lokaci. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Sabiru zai sayi sabon janareta don gujewa matsalar hasken wuta a gaba. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Lokacin da na sami karaya a mota, sai na fahimci muhimmancin adana kuɗi domin buƙatun gaugawa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Idan mutum yana da shirin tanadi mai kyau, zai iya samun sauƙin shawo kan matsalolin kuɗi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ladi ta yi rajistar inshora don samun kariya daga tashin farashi na ba-zata. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Bala ya tafi Abuja domin fara shirin bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yarsa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Nakan ajiye rarar kuɗi domin shawo kan matsalar kuɗin cefane duk wata saboda yawan tashin farashinsu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Mutum zai iya fara tanadi koda da kuɗi kaɗan domin hakan zai taimake sa a gaba. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Idan ana son rage yawan cin bashi, dole a yi tanadi domin abin ka iya faɗowa gagab. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Lokacin hutun shekara, na shirya kallon fina-finai masu ɗauke da farin ciki tare da iyali. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Lokutan bukukuwa suna zama damar yin ayyukan alheri da taimakon marasa ƙarfi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yana da kyau mutum ya san inda zai iya samun taimako idan ya shiga matsala. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Shirya ziyarce-ziryace na daga cikin ayyukan yi lokacin bukukuwan Sallah. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Iyalan Tijjani suna siyan abinci da yawa daga Kasuwar Lagos don gujewa hauhawar farashi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na fahimci cewa ajiyar kuɗi komai ƙanƙantarsa yana taimakawa wajen guje wa wahalar neman bashi. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Aliyu da ‘yan uwansa za su tafi gona don yin shirin bikin Sallah. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
An gayyato makaɗa da mawaƙan ƙasar Nijar, domin wasan sallah ƙarama. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Makarantar su Yusuf tana shirin yin taron karrama manyan malamanta a shekara mai zuwa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na fahimci cewa idan mutum yana da tanadi, zai fi samun kwanciyar hankali a rayuwarsa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Amma ni fa ba na son yawan yawace-yawacen nan gaskiya. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
A riƙa yin la’akari da abubuwan da ka iya tasowa domin kada su zama matsala zuwa gaba. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wani maigadi a Kano ya tara kuɗin euro don matsalolin da za su taso ba-zata. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Za a raba ingarmomin dawakai goma a bikin gasar ƙwallon doki ta bana. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ki zo mu yi ƙunshin sallah saura kwana biyu fa | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Maimuna ta ajiye kuɗi tun da farko don biyan kuɗin makarantar yara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Tsara jerin abubuwan da za a yi a lokacin hutu yana taimakawa wajen rage ɓata lokaci | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ba kowa ke da damar samun taimakon gwamnati ba, idan matsala ta taso masa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Ana buƙatar tsara jadawalin ayyuka domin kowa ya san abin da zai yi a lokacin biki. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Za mu gayyato ‘yan ƙoroso a lokacin bikinmu na shekara-shekara. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wani mutum a Katsina ya sami karyewar kafa, amma ya tanadi kudin asibiti. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na shirya raba kyaututtuka ga makwabta domin nuna haɗin kai a lokacin hutu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Na lura cewa mutane da ke da ajiyar kuɗi ba sa shiga cikin matsala da zarar wani abu ya faru. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Yana da kyau a tsara wasanni masu daɗi domin yara a lokutan bukukuwa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
A shekarar da ta wuce, Maimuna ta rasa aiki ba zato ba tsammani. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Wasu iyalai suna amfani da bukukuwa don koyawa yara al’adunsu. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Mun haɗa jerin sunayen bãƙin da zamu gayyata, domin kada mu manta da kowa. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Tun wuri mun kiwata kajin da za a yi shaglin bikin da su. | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male | |
Borkono yanzu yana arha, gara mu saya kafin lokacin tsadarsa | HAGS1M1 | 15-29 | EV | male |
End of preview. Expand in Data Studio
No dataset card yet
- Downloads last month
- 351