text stringlengths 0 7.06k | length int64 0 2.03k | loss float64 0 10.9 |
|---|---|---|
<translate> Not only should you indentify the truth, but you should also promote insight in the environment in which you live and clarify things to the people around you. <hau>: Ba wai kawai wajibi ne ku gano yanayin ba, face ma dai wajibi ne ku samar da basira cikin yanayin da kuke ciki, wajibi ne ku haskaka yanayi. | 67 | 1.746325 |
<translate> Ba wai kawai wajibi ne ku gano yanayin ba, face ma dai wajibi ne ku samar da basira cikin yanayin da kuke ciki, wajibi ne ku haskaka yanayi. <en>: Not only should you indentify the truth, but you should also promote insight in the environment in which you live and clarify things to the people around you. | 66 | 3.547223 |
<translate> One essential point is that falsity does not always appear in a bare form in front of your eyes, and it is not easy to identify it as falsity. Falsities often enter the arena disguised as truths or half-truths. <hau>: Wani lamari mai muhimmanci shi ne cewa karya da bata ba sa nuna kansu tsirara a gaban mutane ballantana ma mutum ya fahimci cewa wannan bata ce; a mafi yawan lokuta bata ta kan bayyana ne da rigar gaskiya ko kuma wani bangare na gaskiyar. | 105 | 2.674061 |
<translate> Wani lamari mai muhimmanci shi ne cewa karya da bata ba sa nuna kansu tsirara a gaban mutane ballantana ma mutum ya fahimci cewa wannan bata ce; a mafi yawan lokuta bata ta kan bayyana ne da rigar gaskiya ko kuma wani bangare na gaskiyar. <en>: One essential point is that falsity does not always appear in a bare form in front of your eyes, and it is not easy to identify it as falsity. Falsities often enter the arena disguised as truths or half-truths. | 104 | 5.620985 |
<translate> The Commander of the Faithful (a.s.) said that if the truth and falsity entered the arena in a bare form, there would be no disagreements. <hau>: Amirul Muminin (a.s) yana cewa: "Idan da karya a bayyane take ba tare da cakuduwa da (gaskiya) ba, da ba ta buya ga masu nemanta ba. | 79 | 2.292052 |
<translate> Amirul Muminin (a.s) yana cewa: "Idan da karya a bayyane take ba tare da cakuduwa da (gaskiya) ba, da ba ta buya ga masu nemanta ba. <en>: The Commander of the Faithful (a.s.) said that if the truth and falsity entered the arena in a bare form, there would be no disagreements. | 78 | 4.202096 |
<translate> If falsity had been pure and unmixed, it would not be hidden from those who are in search of it. And if the truth had been pure without a mixture of falsity, those who bear hatred towards it would have been silenced." <hau>: Haka nan idan da gaskiya ta kasance a bayyane ba tare da haduwa da karya ba da an rufe bakin wadanda suke adawa da ita" (Nahjul Balaga, huduba ta 50), wato idan da gaskiya da bata sun fito fili ne a fage, to da babu wani sabani da zai saura; kowa yana son gaskiya, sannan kowa kuma yana kin karya da bata. | 133 | 4.147522 |
<translate> Haka nan idan da gaskiya ta kasance a bayyane ba tare da haduwa da karya ba da an rufe bakin wadanda suke adawa da ita" (Nahjul Balaga, huduba ta 50), wato idan da gaskiya da bata sun fito fili ne a fage, to da babu wani sabani da zai saura; kowa yana son gaskiya, sannan kowa kuma yana kin karya da bata. <en>: If falsity had been pure and unmixed, it would not be hidden from those who are in search of it. And if the truth had been pure without a mixture of falsity, those who bear hatred towards it would have been silenced." | 131 | 7.094447 |
<translate> However what is done is that something is taken from here and something from there and the two are mixed, making the truth doubtful to those who seek it. <hau>: To sai dai a kan dauki wani abu daga wannan da wani abu daga wancan sai a hada guda biyun waje guda. A irin wannan yanayi sai Shaidan ya yi nasara a kan abokansa. | 72 | 2.073761 |
<translate> To sai dai a kan dauki wani abu daga wannan da wani abu daga wancan sai a hada guda biyun waje guda. A irin wannan yanayi sai Shaidan ya yi nasara a kan abokansa. <en>: However what is done is that something is taken from here and something from there and the two are mixed, making the truth doubtful to those who seek it. | 71 | 3.820087 |
<translate> They mix up the truth with falsity and do not let falsity be bare and pure. Thus, they mislead their audience. It is necessary to be extremely vigilant in this regard. <hau>: Su kan hada wani bangare na gaskiya da wani bangare na karya waje guda; ba sa barin gaskiya ta bayyana ita kadai, haka nan karya ita kadai; a saboda haka ne mutane su kan fada cikin kuskure; wajibi ne a kula da wannan lamari da kyau. | 96 | 2.837778 |
<translate> Su kan hada wani bangare na gaskiya da wani bangare na karya waje guda; ba sa barin gaskiya ta bayyana ita kadai, haka nan karya ita kadai; a saboda haka ne mutane su kan fada cikin kuskure; wajibi ne a kula da wannan lamari da kyau. <en>: They mix up the truth with falsity and do not let falsity be bare and pure. Thus, they mislead their audience. It is necessary to be extremely vigilant in this regard. | 95 | 5.129831 |
<translate> In global propaganda, today all efforts are focused on complete distortion of the realities of your society and your Islamic government. And they have many propaganda facilities to do this. <hau>: Manufar farfagandar da ake yadawa a duniya a yau ita ce a sauya da kuma bata yanayi na hakika na kasar ku, yanayin al'ummarku da kuma tsarinku na Musulunci. | 73 | 1.964616 |
<translate> Manufar farfagandar da ake yadawa a duniya a yau ita ce a sauya da kuma bata yanayi na hakika na kasar ku, yanayin al'ummarku da kuma tsarinku na Musulunci. <en>: In global propaganda, today all efforts are focused on complete distortion of the realities of your society and your Islamic government. And they have many propaganda facilities to do this. | 72 | 3.87466 |
<translate> Of course there are some people who - knowingly or unknowingly - repeat and reflect their statements inside the country. <hau>: Ko da yake akwai wadansu mutane a cikin gida sun sani ko ba su sani ba da suke sake nanata wadannan maganganu (na makiya) da kuma yada su. | 61 | 1.855471 |
<translate> Ko da yake akwai wadansu mutane a cikin gida sun sani ko ba su sani ba da suke sake nanata wadannan maganganu (na makiya) da kuma yada su. <en>: Of course there are some people who - knowingly or unknowingly - repeat and reflect their statements inside the country. | 60 | 3.219787 |
<translate> There are other factors involved. One is the issue of lack of determination. <hau>: A nan akwai wadansu lamurra; na farkonsu shi ne batun rashin azama da irada. | 38 | 1.146026 |
<translate> A nan akwai wadansu lamurra; na farkonsu shi ne batun rashin azama da irada. <en>: There are other factors involved. One is the issue of lack of determination. | 37 | 1.964616 |
<translate> Some people know the realities, but they fail to make a decision and take action. They do not make up their mind to express what they know. They do not make up their mind to adopt the righteous position and defend the truth. <hau>: Wasu mutanen sun san gaskiya, to sai dai ba sa daukan matsayar aiwatar da ita ne; ba sa daukan matsayar bayyanar da ita; haka nan kuma ba sa yin tsayin daka da tsayawa kyam a kan gaskiya da kuma kare ta. | 99 | 2.674061 |
<translate> Wasu mutanen sun san gaskiya, to sai dai ba sa daukan matsayar aiwatar da ita ne; ba sa daukan matsayar bayyanar da ita; haka nan kuma ba sa yin tsayin daka da tsayawa kyam a kan gaskiya da kuma kare ta. <en>: Some people know the realities, but they fail to make a decision and take action. They do not make up their mind to express what they know. They do not make up their mind to adopt the righteous position and defend the truth. | 98 | 5.293549 |
<translate> Sometimes just because one has made a certain comment, one may want to repeat the same thing persistently and may feel ashamed of taking back one's comment. "May Allah curse obstinate people." There are some people who know the truth, yet they contribute to the enemies' positions. <hau>: Sun fadi wata magana, su na so su ci gaba da tsayawa kyam a kan wannan magana, saboda suna jin kunya wajen janye wannan magana ta su; an ce: "Allah ya la'anci mai taurin kai". Akwai wadansu mutane wadanda sun san me ke gudana, sun san hakikanin abin da ke gudana, amma duk da haka suna taimakawa mahangar da ta saba wa hakan, wato mahangar makiya. | 144 | 4.529531 |
<translate> Sun fadi wata magana, su na so su ci gaba da tsayawa kyam a kan wannan magana, saboda suna jin kunya wajen janye wannan magana ta su; an ce: "Allah ya la'anci mai taurin kai". Akwai wadansu mutane wadanda sun san me ke gudana, sun san hakikanin abin da ke gudana, amma duk da haka suna taimakawa mahangar da ta saba wa hakan, wato mahangar makiya. <en>: Sometimes just because one has made a certain comment, one may want to repeat the same thing persistently and may feel ashamed of taking back one's comment. "May Allah curse obstinate people." There are some people who know the truth, yet they contribute to the enemies' positions. | 143 | 7.749319 |
<translate> Many of the people who got cold feet and gave up used to be extremist revolutionaries one day. But you see now that they are standing for exactly the opposite of what they used to stand for and are serving the anti-revolutionaries. <hau>: Da dama daga cikin mutanen da suka ja da baya, a baya sun kasance ‘yan a mutun wannan juyi; amma a wata rana ku din nan kun ga yadda suka tsaya da dukkan karfinsu wajen fada da hakan da kuma taimaka wa masu adawa da wannan juyin! Hakan saboda wadannan dalilai ne; son zuciya, son rai, da kutsawa cikin son abin duniya. | 124 | 3.983804 |
<translate> Da dama daga cikin mutanen da suka ja da baya, a baya sun kasance ‘yan a mutun wannan juyi; amma a wata rana ku din nan kun ga yadda suka tsaya da dukkan karfinsu wajen fada da hakan da kuma taimaka wa masu adawa da wannan juyin! Hakan saboda wadannan dalilai ne; son zuciya, son rai, da kutsawa cikin son abin duniya. <en>: Many of the people who got cold feet and gave up used to be extremist revolutionaries one day. But you see now that they are standing for exactly the opposite of what they used to stand for and are serving the anti-revolutionaries. | 123 | 6.657866 |
<translate> And the main factor is failing to remember God, neglecting one's duties and ignoring death and the Day of Judgment. <hau>: Babban dalilin hakan shi ne gafala daga ambaton Allah, gafala daga sauke nauyin da ke wuyansu, gafala daga mutuwa da kuma gafala daga ranar lahira. | 64 | 2.073761 |
<translate> Babban dalilin hakan shi ne gafala daga ambaton Allah, gafala daga sauke nauyin da ke wuyansu, gafala daga mutuwa da kuma gafala daga ranar lahira. <en>: And the main factor is failing to remember God, neglecting one's duties and ignoring death and the Day of Judgment. | 63 | 3.383505 |
<translate> Of course some people may make a mistake. It is not right to consider everybody a culprit. I saw some people giving them money as a gift, as a sign of respect. <hau>: Mu dai mun ga wadansu sun zo sun ba su kyauta, a matsayin suna kaunarsu, sun ba su kudi; su kuma sun karbi wadannan kudaden, ba su san cewa hakan wata rashawa ba ce. | 82 | 2.292052 |
<translate> Mu dai mun ga wadansu sun zo sun ba su kyauta, a matsayin suna kaunarsu, sun ba su kudi; su kuma sun karbi wadannan kudaden, ba su san cewa hakan wata rashawa ba ce. <en>: Of course some people may make a mistake. It is not right to consider everybody a culprit. I saw some people giving them money as a gift, as a sign of respect. | 81 | 4.365813 |
<translate> The things that happen in the real world are similar to one another, but it is important to realize whether or not something is a bribe. <hau>: Hakikanin abin da ke faruwa a duniya, abubuwa ne da suka yi kama da junansu; to sai dai fahimtar cewa shin hakan rashawa ce ko kuma a'a, lamari ne mai muhimmanci. | 70 | 2.128334 |
<translate> Hakikanin abin da ke faruwa a duniya, abubuwa ne da suka yi kama da junansu; to sai dai fahimtar cewa shin hakan rashawa ce ko kuma a'a, lamari ne mai muhimmanci. <en>: The things that happen in the real world are similar to one another, but it is important to realize whether or not something is a bribe. | 69 | 3.710942 |
<translate> When you are in a position of power and can do something the way a person wants, that person may naturally come and kiss your hand or offer you money. <hau>: A wani lokaci ka kan sami kanka a wani waje da za ka iya aikata wani abin da ya yi daidai da abin da wani mutum yake so, to ya kan zo ya rungume ka da kuma ba ka kudi. | 77 | 2.346625 |
<translate> A wani lokaci ka kan sami kanka a wani waje da za ka iya aikata wani abin da ya yi daidai da abin da wani mutum yake so, to ya kan zo ya rungume ka da kuma ba ka kudi. <en>: When you are in a position of power and can do something the way a person wants, that person may naturally come and kiss your hand or offer you money. | 76 | 4.09295 |
<translate> Well, this is called bribing, which is haraam. <hau>: To sunan hakan shi ne rashawa; wannan ita ce rashawa ta haramun. | 32 | 0.873163 |
<translate> To sunan hakan shi ne rashawa; wannan ita ce rashawa ta haramun. <en>: Well, this is called bribing, which is haraam. | 31 | 1.63718 |
<translate> They did not realize that they were involved in the kind of fitna about which the Commander of the Faithful (a.s.) said, "Through them Satan's emblems got flying and his standard was raised in vices which trampled the people under their hoofs, and treaded upon them with their feet." Fitna crushes and annihilates those who are in its way. <hau>: A lokacin fitinar nan ma haka lamarin ya kasance. Wasu sun shigo cikin wannan fitina da rikici, ba tare da sun san cewa manufar hakan ita ce kawar da wannan tsari ba; ba su san cewa wannan fitina ita ce fitinar nan da Amirul Muminin (a.s) yake fadn cewa: "Cikin fitinar da ta tattaka mutane da murkushe su da kofatonsu, sannan wadannan (fitinu) suka tsaya da karfinsu" (Nahjul Balaga, huduba ta 2). Fitina tana takawa da murkushe mutanen da suka kasance a karkashin kafafunta. | 207 | 6.166711 |
<translate> A lokacin fitinar nan ma haka lamarin ya kasance. Wasu sun shigo cikin wannan fitina da rikici, ba tare da sun san cewa manufar hakan ita ce kawar da wannan tsari ba; ba su san cewa wannan fitina ita ce fitinar nan da Amirul Muminin (a.s) yake fadn cewa: "Cikin fitinar da ta tattaka mutane da murkushe su da kofatonsu, sannan wadannan (fitinu) suka tsaya da karfinsu" (Nahjul Balaga, huduba ta 2). Fitina tana takawa da murkushe mutanen da suka kasance a karkashin kafafunta. <en>: They did not realize that they were involved in the kind of fitna about which the Commander of the Faithful (a.s.) said, "Through them Satan's emblems got flying and his standard was raised in vices which trampled the people under their hoofs, and treaded upon them with their feet." Fitna crushes and annihilates those who are in its way. | 206 | 10.859961 |
<translate> Somebody said something, and they repeated it. <hau>: Wani mutum (a wancan bangaren) ya fadi wata magana, su kuma suka ci gaba da nanata ta. | 35 | 1.255171 |
<translate> Wani mutum (a wancan bangaren) ya fadi wata magana, su kuma suka ci gaba da nanata ta. <en>: Somebody said something, and they repeated it. | 34 | 1.800898 |
<translate> Therefore, it is not right to hand out the same punishment to everybody. <hau>: A saboda haka babu yadda za a yi wa dukkaninsu hukumci guda. | 33 | 0.873163 |
<translate> A saboda haka babu yadda za a yi wa dukkaninsu hukumci guda. <en>: Therefore, it is not right to hand out the same punishment to everybody. | 32 | 1.691753 |
<translate> The punishment of a warring enemy is different from the punishment of an unaware person. <hau>: Hukumcin makiya ya banbanta da na wanda ya gafala. | 35 | 0.873163 |
<translate> Hukumcin makiya ya banbanta da na wanda ya gafala. <en>: The punishment of a warring enemy is different from the punishment of an unaware person. | 34 | 1.800898 |
<translate> Of course unaware people should be awakened. <hau>: Ko da yake wajibi ne shi ma wanda ya gafalan ya farka. | 27 | 0.873163 |
<translate> Ko da yake wajibi ne shi ma wanda ya gafalan ya farka. <en>: Of course unaware people should be awakened. | 26 | 1.364317 |
<translate> What I want to tell you dear youth is that you should be vigilant, be present on the scene and base your actions on insight in order to be able to build Islamic Iran, fulfill your duties towards Islam and make your nation, your dear homeland and your history glorious. Today if somebody makes efforts for the glory of Islamic Iran, he has served his homeland, his nation, his history and dear Islam which is a source of salvation for humanity. <hau>: Ina so in sanar da ku, Ya ku matasa; ku din nan don ku sami damar gina kasar Iran, wato don ku daukaka wannan al'umma da wannan kasa mai girma da kuma tarihinsu, wajibi ne ku aiwatar da nauyin da ke wuyanku na daukaka Musulunci - wanda a yau idan har wani mutum ya aikata wani abu wajen daukakar kasar Musulunci ta Iran, to ya yi hidima ne wa kasarsa da kuma al'ummarsa da kuma tarihinsa, haka nan kuma ga Musulunci mai girma da ‘yantar da bil'adama - wajibi ne ku farka, wajibi ne ku yi taka tsantsan, wajibi ne ku zamanto a fage, haka nan kuma wajibi ne ku sanya basira ta zamanto ita ce ma'auninku. | 236 | 5.784702 |
<translate> Ina so in sanar da ku, Ya ku matasa; ku din nan don ku sami damar gina kasar Iran, wato don ku daukaka wannan al'umma da wannan kasa mai girma da kuma tarihinsu, wajibi ne ku aiwatar da nauyin da ke wuyanku na daukaka Musulunci - wanda a yau idan har wani mutum ya aikata wani abu wajen daukakar kasar Musulunci ta Iran, to ya yi hidima ne wa kasarsa da kuma al'ummarsa da kuma tarihinsa, haka nan kuma ga Musulunci mai girma da ‘yantar da bil'adama - wajibi ne ku farka, wajibi ne ku yi taka tsantsan, wajibi ne ku zamanto a fage, haka nan kuma wajibi ne ku sanya basira ta zamanto ita ce ma'auninku. <en>: What I want to tell you dear youth is that you should be vigilant, be present on the scene and base your actions on insight in order to be able to build Islamic Iran, fulfill your duties towards Islam and make your nation, your dear homeland and your history glorious. Today if somebody makes efforts for the glory of Islamic Iran, he has served his homeland, his nation, his history and dear Islam which is a source of salvation for humanity. | 235 | 10.859961 |
<translate> Take care not to suffer from lack of insight. <hau>: Ku lura sosai kada ku fuskanci matsalar rashin basira. | 23 | 0.600299 |
<translate> Ku lura sosai kada ku fuskanci matsalar rashin basira. <en>: Take care not to suffer from lack of insight. | 22 | 1.146026 |
<translate> Try to identify the enemy. <hau>: Ku fahimci makiya. | 14 | 0.327436 |
<translate> Ku fahimci makiya. <en>: Try to identify the enemy. | 13 | 0.654872 |
<translate> Do not let the appearance of the enemy deceive you. <hau>: Kada ku fada tarkon zahirin makiya. | 26 | 0.654872 |
<translate> Kada ku fada tarkon zahirin makiya. <en>: Do not let the appearance of the enemy deceive you. | 25 | 1.309744 |
<translate> Materialism, materialistic tendencies, materialistic thought and materialistic civilization are your enemies and the enemies of humanity. <hau>: Tunani na abin duniya, akidar abin duniya, wayewa irin ta abin duniya, dukkanin wadannan abubuwan makiya bil'adama ne, don haka makiyan ku ne su. | 61 | 1.855471 |
<translate> Tunani na abin duniya, akidar abin duniya, wayewa irin ta abin duniya, dukkanin wadannan abubuwan makiya bil'adama ne, don haka makiyan ku ne su. <en>: Materialism, materialistic tendencies, materialistic thought and materialistic civilization are your enemies and the enemies of humanity. | 60 | 3.219787 |
<translate> The western world achieved superior knowledge and technology two to three centuries ago, and it found a way to accumulate wealth. Different social schools were created. <hau>: Kasashen yammaci tun daga karnoni biyu zuwa uku da suka gabata suka sami ilimi sama da sauran mutane don haka suka sami hanyar tattara dukiya mai yawan gaske. | 64 | 1.746325 |
<translate> Kasashen yammaci tun daga karnoni biyu zuwa uku da suka gabata suka sami ilimi sama da sauran mutane don haka suka sami hanyar tattara dukiya mai yawan gaske. <en>: The western world achieved superior knowledge and technology two to three centuries ago, and it found a way to accumulate wealth. Different social schools were created. | 63 | 3.383505 |
<translate> Different philosophical and social thoughts came into being - liberalism which was based on humanistic thought, democracy and similar other things. <hau>: Daga nan ne akidu daban-daban na zamantakewa suka kunno kai, tunani da akidu daban-daban na falsafar zamantakewa suka bayyana - akidar sassauci da ta ginu bisa tunani na dan'adam, tunani na demokradiyya da makamantan hakan - manufarsu ko kuma manufar mutanen da suke kokarin yada wannan tunani ita ce ko za su sami damar kai dan'adam zuwa ga jin dadi da kwanciyar hankali; to sai dai abin da aka cimma a zahiri shi ne akasin hakan. | 123 | 5.238976 |
<translate> Daga nan ne akidu daban-daban na zamantakewa suka kunno kai, tunani da akidu daban-daban na falsafar zamantakewa suka bayyana - akidar sassauci da ta ginu bisa tunani na dan'adam, tunani na demokradiyya da makamantan hakan - manufarsu ko kuma manufar mutanen da suke kokarin yada wannan tunani ita ce ko za su sami damar kai dan'adam zuwa ga jin dadi da kwanciyar hankali; to sai dai abin da aka cimma a zahiri shi ne akasin hakan. <en>: Different philosophical and social thoughts came into being - liberalism which was based on humanistic thought, democracy and similar other things. | 122 | 6.603292 |
<translate> Yesterday I read in a newspaper that according to American sources the US carried out 80 coups in the world from 1940s to 1990s - that is to say, within fifty years. <hau>: A jiya din nan na ke karantawa cikin jarida inda aka nakalto daga wasu majiyoyin Amurka cewa daga shekarun 1940 zuwa 1990 - wato tsawon shekaru hamsin - Amurka ta shirya juyin mulkin soja guda tamanin a duniya! | 81 | 2.346624 |
<translate> A jiya din nan na ke karantawa cikin jarida inda aka nakalto daga wasu majiyoyin Amurka cewa daga shekarun 1940 zuwa 1990 - wato tsawon shekaru hamsin - Amurka ta shirya juyin mulkin soja guda tamanin a duniya! <en>: Yesterday I read in a newspaper that according to American sources the US carried out 80 coups in the world from 1940s to 1990s - that is to say, within fifty years. | 80 | 4.311241 |
<translate> You see the brutality of those who have achieved the peaks of wealth, technology, weapons, manufacture of military equipment and different other things. <hau>: Ku duba ku ga mutanen da suka kai wani koli na dukiya da fasaha da makamai da kere-kere, to amma wannan shi ne irin rashin imani da dabbancinsu. | 65 | 1.964616 |
<translate> Ku duba ku ga mutanen da suka kai wani koli na dukiya da fasaha da makamai da kere-kere, to amma wannan shi ne irin rashin imani da dabbancinsu. <en>: You see the brutality of those who have achieved the peaks of wealth, technology, weapons, manufacture of military equipment and different other things. | 64 | 3.438078 |
<translate> Murder is something ordinary for them. They kill "in cold blood" - this phrase is in western literature. <hau>: Zubar da jinin mutane ya zamanto wani karamin abu a wajensu; kamar yadda suke fadi kisan gilla na keta. | 48 | 1.364317 |
<translate> Zubar da jinin mutane ya zamanto wani karamin abu a wajensu; kamar yadda suke fadi kisan gilla na keta. <en>: Murder is something ordinary for them. They kill "in cold blood" - this phrase is in western literature. | 47 | 2.510343 |
<translate> This is a sign of complete cruelty. <hau>: Mutanen yammaci su kan fadi cewa an kashe wane kisa ta keta; hakan lamari ne da ke nuni da kekashewar zuciya. | 38 | 1.473462 |
<translate> Mutanen yammaci su kan fadi cewa an kashe wane kisa ta keta; hakan lamari ne da ke nuni da kekashewar zuciya. <en>: This is a sign of complete cruelty. | 37 | 1.964616 |
<translate> This is the case not only in Afghanistan, Iraq and other places they have occupied, but also in their own country. <hau>: Ba wai kawai a Afghanistan da Iraki da sauran yankunan da suke karkashin mamayarsu ba, a cikin al'ummarsu ma haka suke yi. | 54 | 1.528035 |
<translate> Ba wai kawai a Afghanistan da Iraki da sauran yankunan da suke karkashin mamayarsu ba, a cikin al'ummarsu ma haka suke yi. <en>: This is the case not only in Afghanistan, Iraq and other places they have occupied, but also in their own country. | 53 | 2.837779 |
<translate> Go to their literature, which shows the realities of their life. <hau>: Ku koma ga irin maganganu da al'adunsu ku gani, wacce take nuni da hakikanin rayuwarsu. | 35 | 1.036881 |
<translate> Ku koma ga irin maganganu da al'adunsu ku gani, wacce take nuni da hakikanin rayuwarsu. <en>: Go to their literature, which shows the realities of their life. | 34 | 1.800898 |
<translate> Their art and literature shows what is happening in their lives. <hau>: Rubuce-rubuce da al'adunsu suna nuni ne da irin abubuwan da ke faruwa cikin rayuwarsu. | 34 | 1.091453 |
<translate> Rubuce-rubuce da al'adunsu suna nuni ne da irin abubuwan da ke faruwa cikin rayuwarsu. <en>: Their art and literature shows what is happening in their lives. | 33 | 1.746325 |
<translate> Murder is extremely easy for them. <hau>: Zubar da jinin mutum wani aiki ne mai saukin gaske a wajensu. | 25 | 0.873163 |
<translate> Zubar da jinin mutum wani aiki ne mai saukin gaske a wajensu. <en>: Murder is extremely easy for them. | 24 | 1.255171 |
<translate> On the other hand, in their communities and among their youth, one can see depression, disappointment with life and revolt against social norms. <hau>: A bangare guda ma cikin al'ummarsu, a cikin matasansu, a fili a ke iya ganin damuwa, yanke kauna daga rayuwa da makamantan haka. | 62 | 1.746325 |
<translate> A bangare guda ma cikin al'ummarsu, a cikin matasansu, a fili a ke iya ganin damuwa, yanke kauna daga rayuwa da makamantan haka. <en>: On the other hand, in their communities and among their youth, one can see depression, disappointment with life and revolt against social norms. | 61 | 3.27436 |
<translate> These are what have been experienced by western systems and schools of thought. And these are all caused by the fact that they have drifted away from religion, spirituality and God. <hau>: Ummul aba'isin din dukkanin wadannan abubuwa shi ne cewa su din nan sun yi nisa da addini, sun yi nisa da ababen da suke kusata mutum da Ubangiji, sun yi nisa da Ubangiji. | 79 | 2.237479 |
<translate> Ummul aba'isin din dukkanin wadannan abubuwa shi ne cewa su din nan sun yi nisa da addini, sun yi nisa da ababen da suke kusata mutum da Ubangiji, sun yi nisa da Ubangiji. <en>: These are what have been experienced by western systems and schools of thought. And these are all caused by the fact that they have drifted away from religion, spirituality and God. | 78 | 4.202096 |
<translate> Therefore, their behavior is the enemy of humanity. <hau>: A saboda haka halayensu suka zamanto masu adawa da bil'adama. | 26 | 0.764017 |
<translate> A saboda haka halayensu suka zamanto masu adawa da bil'adama. <en>: Therefore, their behavior is the enemy of humanity. | 25 | 1.309744 |
<translate> Today you are moving in the opposite direction. <hau>: To ku din nan a yau kuna tafiya ne akasin hakan. | 24 | 0.709445 |
<translate> To ku din nan a yau kuna tafiya ne akasin hakan. <en>: Today you are moving in the opposite direction. | 23 | 1.200599 |
<translate> You want to achieve knowledge through divine thought. You want to make use of natural and human facilities in order to bring about material and spiritual benefits for your nation, other nations and humanity. <hau>: Ku din na kuna so ku yi amfani da ilimi ne ta hanyar da ta yi daidai da koyarwa ta Ubangiji; ku din nan kuna so ne ku tattaro albarkatu na dabi'a da na mutane wajen amfani na duniya da lahira ga al'ummar ku da sauran al'ummomi na duniya, don amfani dukkanin bil'adama. | 98 | 3.219787 |
<translate> Ku din na kuna so ku yi amfani da ilimi ne ta hanyar da ta yi daidai da koyarwa ta Ubangiji; ku din nan kuna so ne ku tattaro albarkatu na dabi'a da na mutane wajen amfani na duniya da lahira ga al'ummar ku da sauran al'ummomi na duniya, don amfani dukkanin bil'adama. <en>: You want to achieve knowledge through divine thought. You want to make use of natural and human facilities in order to bring about material and spiritual benefits for your nation, other nations and humanity. | 97 | 5.238976 |
<translate> This movement will achieve success. It will continue. This movement is the opposite of the wrong and misguided two- or three-century-long movement started by the west. <hau>: Mahangarku mahanga ce ta Ubangiji; hakan lamari ne da zai yi nasara, hakan zai ci gaba; wannan shi ne kishiyar wannan yunkuri da kokari da ke cike da kuskure na karnoni da kasashen yammaci suke yi. | 83 | 2.619488 |
<translate> Mahangarku mahanga ce ta Ubangiji; hakan lamari ne da zai yi nasara, hakan zai ci gaba; wannan shi ne kishiyar wannan yunkuri da kokari da ke cike da kuskure na karnoni da kasashen yammaci suke yi. <en>: This movement will achieve success. It will continue. This movement is the opposite of the wrong and misguided two- or three-century-long movement started by the west. | 82 | 4.420386 |
<translate> This movement is an auspicious movement, and it will continue. <hau>: Wannan shi ne yunkurin da ke cike da albarka wanda kuma za a ci gaba da shi. | 35 | 1.036881 |
<translate> Wannan shi ne yunkurin da ke cike da albarka wanda kuma za a ci gaba da shi. <en>: This movement is an auspicious movement, and it will continue. | 34 | 1.800898 |
<translate> They should ask God for assistance. They should move forward with insight. Then they will gain the appropriate means to confront the wrong methods that are prevalent in the world, and by Allah's favor, they will achieve all the ideals and wishes delineated by Islam and the Revolution. <hau>: Wajibi ne matashi musulmi na Iran ya shirya kansa; ya tsara kansa; cikin tafarkin ci gaba ya dogara da Allah; ku nemi taimako daga wajen Allah; ku ci gaba ta hanyar riko da basira; a wannan lokacin ne za ku sami hanyar da ta dace wajen fada da wannan mummunar hanya da take iko a kasashen yammaci, sannan kuma da yardar Allah za ku sami damar isa ga dukkanin fatan da Musulunci da juyin juya halin Musulunci suka tsara. | 148 | 4.91154 |
<translate> Wajibi ne matashi musulmi na Iran ya shirya kansa; ya tsara kansa; cikin tafarkin ci gaba ya dogara da Allah; ku nemi taimako daga wajen Allah; ku ci gaba ta hanyar riko da basira; a wannan lokacin ne za ku sami hanyar da ta dace wajen fada da wannan mummunar hanya da take iko a kasashen yammaci, sannan kuma da yardar Allah za ku sami damar isa ga dukkanin fatan da Musulunci da juyin juya halin Musulunci suka tsara. <en>: They should ask God for assistance. They should move forward with insight. Then they will gain the appropriate means to confront the wrong methods that are prevalent in the world, and by Allah's favor, they will achieve all the ideals and wishes delineated by Islam and the Revolution. | 147 | 7.967609 |
<translate> Leader's sermons at Eid ul-Fitr prayers - Khamenei.ir <hau>: Hudubar Jagora Imam Khamenei Yayin Sallar Idin Karamar Salla Ta Shekarar 1436 | 37 | 0.982308 |
<translate> Hudubar Jagora Imam Khamenei Yayin Sallar Idin Karamar Salla Ta Shekarar 1436 <en>: Leader's sermons at Eid ul-Fitr prayers - Khamenei.ir | 35 | 1.855471 |
<translate> The following is the full text of the sermons delivered on July 18, 2015 by Ayatollah Khamenei, the Leader of the Islamic Revolution, at the Eid ul-Fitr prayers in Tehran. <hau>: Shimfida: Abin da ke biye fassarar hudubar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi ne yayin da ya jagoranci sallar idin karamar salla a Tehran, a ranar Asabar 18, Yulin, 2015: | 89 | 2.510343 |
<translate> Shimfida: Abin da ke biye fassarar hudubar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi ne yayin da ya jagoranci sallar idin karamar salla a Tehran, a ranar Asabar 18, Yulin, 2015: <en>: The following is the full text of the sermons delivered on July 18, 2015 by Ayatollah Khamenei, the Leader of the Islamic Revolution, at the Eid ul-Fitr prayers in Tehran. | 88 | 4.747822 |
<translate> In the Name of Allah, the Beneficent, the Merciful <hau>: Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai | 27 | 0.491154 |
<translate> Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai <en>: In the Name of Allah, the Beneficent, the Merciful | 25 | 1.309744 |
<translate> All praise is due to Allah, Lord of the Worlds. <hau>: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. | 26 | 0.654872 |
<translate> Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. <en>: All praise is due to Allah, Lord of the Worlds. | 25 | 1.309744 |
<translate> Dear God, accept what the people of Iran have done with Your mercy and kindness. <hau>: Ya Ubangiji Allah! Albarkacin rahama da tausayinka, Ka karba wa al'ummar Iran. | 39 | 1.091453 |
<translate> Ya Ubangiji Allah! Albarkacin rahama da tausayinka, Ka karba wa al'ummar Iran. <en>: Dear God, accept what the people of Iran have done with Your mercy and kindness. | 38 | 2.019189 |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.