audio audioduration (s) 3.29 363 | speaker_id stringclasses 386
values | audio_id stringlengths 23 32 | transcript stringlengths 38 4.31k | audio_path stringlengths 34 43 | gender stringclasses 2
values | age_group stringclasses 5
values | education stringclasses 3
values | duration float64 3.29 363 | language stringclasses 1
value | snr int64 40 40 | domain stringclasses 3
values |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
HT2M3 | hau_m_HT2M3_ev_read_128 | Abu ne mai kyau a kullum ka yi tunanin me za ka yi. | audio/hau_m_HT2M3_ev_read_128.flac | male | 30-45 | Tertiary | 4.414 | hausa | 40 | EV | |
HS3F2 | hau_f_HS3F2_ev_read_189 | Mu kuwa Musulmi mukan je Makka domin aikin Hajji ko Umara. | audio/hau_f_HS3F2_ev_read_189.flac | female | 46-60 | Secondary | 6.594 | hausa | 40 | EV | |
HS2F1 | hau_f_HS2F1_ev_read_320 | Yau za a rufe rajistar makarantar koyon sana'o'i a ƙauyen nasu | audio/hau_f_HS2F1_ev_read_320.flac | female | 30-45 | Secondary | 5.793 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_196 | hau_f_196_ev_spontaneous_014 | Akwai nau’in maƙwabtaka kala-kala daban-daban. Idan har kana tare, za ka kallesu, kowa da kalan halinshi, kowa da irin rayuwarsa. Na farko, akwai maƙwabcin da idan har yaji acikin gida ana shi, ba za iya haƙuri ba. Ya dakata, to kawai zai shigo kai tsaye, domin zuwa yayi ceto. Kalmar wannan maƙwabcin zai ke faɗa: “Ayi ... | audio/hau_f_196_ev_spontaneous_014.flac | female | 30-45 | Primary | 101.84 | hausa | 40 | EV | |
HP1F2 | hau_f_HP1F2_ev_read_416 | Shiru-shirun Amina da kunyarta, ya sa na ji ina sonta. | audio/hau_f_HP1F2_ev_read_416.flac | female | 15-29 | Primary | 5.534 | hausa | 40 | EV | |
HM4F1 | hau_f_HM4F1_ev_read_342 | A al’adarmu, ana sa ran mutum ya kasance mai kyauta, amma yana da kyau a san iyaka. | audio/hau_f_HM4F1_ev_read_342.flac | female | 60+ | Primary | 8.674 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_810 | hau_m_810_ag_spontaneous_033 | A gaskiya yanayin abinci haka yana iya zama damuwa duk da dai akan yi noma a nan da dama, za ka samu a ɓangaren ƙauyuka ana yin noman. In an yi noman, an samu an girbe wa’incan kayayyakin gona, sun zo gida. Ana farko manomi yana buƙatan wasu kalan abinci. A na biyu in manomi yana da iyali, iyali suna buƙatar kaya. Buƙa... | audio/hau_m_810_ag_spontaneous_033.flac | male | 30-45 | Tertiary | 99 | hausa | 40 | AG | |
HT1M3 | hau_m_HT1M3_ev_read_552 | Yaya gidan naku? Da fatan ba wata matsala ta wutar lantarki. | audio/hau_m_HT1M3_ev_read_552.flac | male | 15-29 | Tertiary | 4.794 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_1560 | hau_f_1560_he_spontaneous_006 | Dangantakar da ke tsakanin samun magungunan hana ɗaukar ciki da sauran ma da sauran [?] lapiya da sauran harkokin lapiyar haihuwa kamar zubar da ciki samun [?] samun magungunan hana ɗaukar ciki [?] da sauran ayyukan kula da [?] lafiyar haihuwa kamar shawara da [?] da gwada gwaje-gwaji [?] gwaje-gwaje yana da matuƙar ma... | audio/hau_f_1560_he_spontaneous_006.flac | female | 46-60 | Secondary | 160.56 | hausa | 40 | HE | |
HP3M1 | hau_m_HP3M1_ev_read_266 | Ka yi talla ga kamfanonin gida ta hanyar raba bayanai a kafafen sada zumunta. | audio/hau_m_HP3M1_ev_read_266.flac | male | 46-60 | Primary | 10.394 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_249 | hau_f_249_he_spontaneous_015 | Yadda anti bayatic ke aiki, da kuma inda ake samun su. Anti bayotic magunguna ne da ake samunsu, don kasha kwayoyin cuta da cututtuka. An yi su ne domin kashe cuta, kamar su bacteriya, da su fungus idan aka samu mutum da shi a jiki. Anti bayotic magani ne mai ƙarfi wanda yake taimakawa wajen in mutum bai da lafiya, cut... | audio/hau_f_249_he_spontaneous_015.flac | female | 30-45 | Primary | 109.96 | hausa | 40 | HE | |
HT2F2 | hau_f_HT2F2_ev_read_354 | Kowace shekara, muna tuna ranar haihuwar ‘ya’yanmu domin tunawa da farkon zuwansu duniya. | audio/hau_f_HT2F2_ev_read_354.flac | female | 30-45 | Tertiary | 7.814 | hausa | 40 | EV | |
HS2M2 | hau_m_HS2M2_ev_read_508 | Ba sai ka biya ko kobo ba, idan kamfanin da ya sayar ma kaya ya zo gida gyarawa a cikin watanni shida. | audio/hau_m_HS2M2_ev_read_508.flac | male | 30-45 | Secondary | 8.554 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_912 | hau_f_912_ev_spontaneous_037 | Barka war haka! A wannan hoto, an gwado mana hoto ne wato na yanda ake wato kiɗa na ganga. Kamar yadda muka sani, ganga akan kaɗa shi ne a lokaci daban-daban. Yayin da aka gwado yara suke rawa, suke murna, suke tsalle-tsalle a wannan wurin mai kiɗa. Kamar yadda muke gani, shi wannan mai ganga yana sanye ne wato da kaya... | audio/hau_f_912_ev_spontaneous_037.flac | female | 15-29 | Tertiary | 180.72 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_134 | hau_m_134_ag_spontaneous_005 | daga ƙarshe kankana kenan wannan shi wannan shi ma kayan gona ne akan shuka shi ya fito har a dashe shi a cire shi a kan ɓare shi kafin a sha yana da ƙwallaye a cikinsa wasu sukan ci shi da ƙwallon shi wasu kuma sukan cire ƙwallayen kafin su ci wasu kam sukan sarrafa shi ta hanya kala kala wasu kan sarrafa shi tare da ... | audio/hau_m_134_ag_spontaneous_005.flac | male | 15-29 | Tertiary | 92.16 | hausa | 40 | AG | |
HS1F4 | hau_f_HS1F4_ev_read_124 | Ba ya wasa da cikinsa, inda yake cin abinci da zarar ya ji yunwa. | audio/hau_f_HS1F4_ev_read_124.flac | female | 15-29 | Secondary | 5.754 | hausa | 40 | EV | |
HP1M3 | hau_m_HP1M3_ev_read_015 | Taron iyali ya zama abu muhummi don karanta tarihin magabata . | audio/hau_m_HP1M3_ev_read_015.flac | male | 15-29 | Primary | 5.734 | hausa | 40 | EV | |
HS3F2 | hau_f_HS3F2_ev_read_561 | A kowace shekara, ana gudanar da bukukuwan gargajiya lokuta daban-daban domin tunawa da tsofaffin al'adu. | audio/hau_f_HS3F2_ev_read_561.flac | female | 46-60 | Secondary | 11.394 | hausa | 40 | EV | |
HP3M1 | hau_m_HP3M1_ev_read_200 | Shirya liyafa yana bukatar a tsara wuri da lokacin da ya dace. | audio/hau_m_HP3M1_ev_read_200.flac | male | 46-60 | Primary | 7.394 | hausa | 40 | EV | |
HT1F3 | hau_f_HT1F3_ev_read_271 | Dole ne mutane su sami sahihiyar hanyar bayyana ra’ayinsu ba tare da fuskantar matsala ba. | audio/hau_f_HT1F3_ev_read_271.flac | female | 15-29 | Tertiary | 7.894 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_261 | hau_m_261_ev_spontaneous_032 | A kalmar Hausa, wannan yana nufin ɗeban ruwa a burtsatsai ko ruwan burtsatsai. Kaman yadda muka sani ne, shi ruwan burtsatsai dai ya fi yawa a ƙautuka. Ƙungiyoyi kaman irin ƙungiyoyi wanda ba na gwanti ba sun je sun giggina shi a wannan wurare, saboda wannan mutanen wurare ba su da ruwan sha, an gina musu da dama wanna... | audio/hau_m_261_ev_spontaneous_032.flac | male | 15-29 | Secondary | 113.78 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_091 | hau_m_091_ag_spontaneous_007 | Wannan shi ne a Hausance muke ƙiransa da aure, ko kuma a ce haɗi. Ana ce mar haɗi ko aure. Wannan hanya ce wacce ake samar da, wani nau’in tsiri, Wanda daga jikin wani da wani ake ɗaukan sa a haɗa su, don samar da wadatacce ko kyakykyawar amfani amfani. Mafi yawanci ana yin sa a mangwaro, leman tsami, leman zaƙi, da da... | audio/hau_m_091_ag_spontaneous_007.flac | male | 15-29 | Primary | 99.58 | hausa | 40 | AG | |
HT2M1 | hau_m_HT2M1_ev_read_004 | Aminu ya kammala karatun digiri na uku a wannan sabuwar shekara. | audio/hau_m_HT2M1_ev_read_004.flac | male | 30-45 | Tertiary | 5.274 | hausa | 40 | EV | |
HAGT1F1 | hau_f_HAGT1F1_ev_spontaneous_174 | Zaluncin ‘yan sanda yana haifar da fargaba a cikin al’umma, da kuma rage amincewar mutane da doka. | audio/hau_f_HAGT1F1_ev_spontaneous_174.flac | female | 15-29 | Tertiary | 8.2 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_646 | hau_f_646_ev_spontaneous_027 | Banbanci tsakanin ɓangaren gwamnati da ɓangaren masana’antu, a cikin tattalin arzikin kowace kasa akwai manyan ɓangarori guda biyu dake tafiyar da ayyukan yau da kullum ɓangaren gwamnati da ɓangaren masu zaman kansu kowanan su yana da rawar da yake takawa da fa’idoji da kuma kalubale, mene ne ɓangaren gwamtani? ɓangare... | audio/hau_f_646_ev_spontaneous_027.flac | female | 15-29 | Secondary | 117 | hausa | 40 | EV | |
HAGT2M1 | hau_m_HAGT2M1_ev_spontaneous_163 | Ina da ran mallakar kamfanin ƙera mota nan da shekara hamsin. | audio/hau_m_HAGT2M1_ev_spontaneous_163.flac | male | 30-45 | Tertiary | 4.234 | hausa | 40 | EV | |
HT1M1 | hau_m_HT1M1_ev_read_252 | Coci-coci suna taimakawa wajen bayar da tallafi ga marasa galihu da mabuƙata. | audio/hau_m_HT1M1_ev_read_252.flac | male | 15-29 | Tertiary | 6.574 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_031 | hau_f_031_ag_spontaneous_019 | tantance amfanin gona bayan girbi yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da ingancin amfanin gona da aka noma da kuma rage asara da kuma samun riba mai yawa wannan hoton muna ganin yanda ake tantance tumatir bayan girba shi wanda yana da matuƙar muhimmanci wannan matakin na tantance tumatir yana taimakawa wajen cire... | audio/hau_f_031_ag_spontaneous_019.flac | female | 30-45 | Tertiary | 111.72 | hausa | 40 | AG | |
HS3F2 | hau_f_HS3F2_ev_read_522 | Muna ziyarar yawon salla gidajen ƴan'uwa da abokan arziki duk salla. | audio/hau_f_HS3F2_ev_read_522.flac | female | 46-60 | Secondary | 8.434 | hausa | 40 | EV | |
HAGS1M1 | hau_m_HAGS1M1_ev_spontaneous_202 | A watan da ya gabata, na yi gaggawar gyara famfon gidanmu da ya lalace. | audio/hau_m_HAGS1M1_ev_spontaneous_202.flac | male | 15-29 | Secondary | 7.694 | hausa | 40 | EV | |
HT1M3 | hau_m_HT1M3_ev_read_129 | Yayin tafiya da jirgin ƙasa, mutane da dama na karanta jaridu ko mujallu. | audio/hau_m_HT1M3_ev_read_129.flac | male | 15-29 | Tertiary | 5.153 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_481 | hau_m_481_ev_spontaneous_022 | Barkanmu dai wannan biidiyo ya gwado mana ne ko kuma ince yana magana ne akan wato ilimi da ake zuwa makarantu a koyesu da kuma ilimi na raayuwa. Wato shi ilimi da ake zuwa a koye shi a makaranta ko kuma ince da ake koya a makarantu ya shafi wato makarantu na firamari makarantu na sakandare makarantu na jami’a da dai s... | audio/hau_m_481_ev_spontaneous_022.flac | male | 30-45 | Primary | 92.89 | hausa | 40 | EV | |
HM4F2 | hau_f_HM4F2_ev_read_220 | Fatima tana amfani da dabarun sarrafa lokaci don kula da iyali ba tare da gajiya ba. | audio/hau_f_HM4F2_ev_read_220.flac | female | 60+ | Primary | 8.514 | hausa | 40 | EV | |
HM4M2 | hau_m_HM4M2_ev_read_117 | Don mutum zai iya ɓata lokacinsa a banza kuma ba riba. | audio/hau_m_HM4M2_ev_read_117.flac | male | 60+ | Tertiary | 7.454 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_959 | hau_f_959_ev_spontaneous_027 | Yawwa kamar yanda ajiya don gaba don jin daɗin yau da kullum ba tare da jin damuwa game da kuɗi ba yana iya zama ƙalubale amma yana yiwuwa da wasu dabaru masu sauƙi kamar ƙirƙiran kasafin kuɗi tsara kasafin kudi wanda zai ware wani kaso na kuɗin shiga don ajiya da kuma kasafin kudi wannan yana tabbatar da cewa kana iya... | audio/hau_f_959_ev_spontaneous_027.flac | female | 46-60 | Tertiary | 153.3 | hausa | 40 | EV | |
HAGT2F1 | hau_f_HAGT2F1_ev_spontaneous_551 | Alƙalin ya raba auren wasu ma'aurata, don ya aure matar. | audio/hau_f_HAGT2F1_ev_spontaneous_551.flac | female | 30-45 | Tertiary | 7.554 | hausa | 40 | EV | |
HP1F3 | hau_f_HP1F3_ev_read_590 | Nijeriya tana samun kashi sittin na abinci daga arewacin ƙasar. | audio/hau_f_HP1F3_ev_read_590.flac | female | 15-29 | Primary | 7.374 | hausa | 40 | EV | |
HAGT2M1 | hau_m_HAGT2M1_ev_spontaneous_552 | Yara sun fi girma cikin fahimta idan aka koya musu cewa bambanci bai zama matsala ba. | audio/hau_m_HAGT2M1_ev_spontaneous_552.flac | male | 30-45 | Tertiary | 5.754 | hausa | 40 | EV | |
HAGT2M3 | hau_m_HAGT2M3_ev_spontaneous_437 | Yan gudun hijira sun nemi masu hannu da shuni su tallafa musu. | audio/hau_m_HAGT2M3_ev_spontaneous_437.flac | male | 30-45 | Tertiary | 6.3 | hausa | 40 | EV | |
HP1M3 | hau_m_HP1M3_ev_read_361 | Maryam za ta tara kudi na tsawon shekaru don fara karatu a ƙetare. | audio/hau_m_HP1M3_ev_read_361.flac | male | 15-29 | Primary | 6.054 | hausa | 40 | EV | |
HAGT2F1 | hau_f_HAGT2F1_ev_spontaneous_135 | Audu ya ga Ali ya sayo mota, shi ma ya dage sai ya saya. | audio/hau_f_HAGT2F1_ev_spontaneous_135.flac | female | 30-45 | Tertiary | 8.874 | hausa | 40 | EV | |
HS3F1 | hau_f_HS3F1_ev_read_424 | Dafa ƙirji da tafin hannu tare da ɗan sunkuyawa gaisuwa ce ga mutanen China | audio/hau_f_HS3F1_ev_read_424.flac | female | 46-60 | Secondary | 12.474 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_571 | hau_m_571_he_spontaneous_033 | Covid 19, ana yaɗuwa ko kuma ana yaɗa ta farko daga mutum zuwa mutum ta hanyan ɗigon numfashi, hulɗa da gurɓataccen wuri da kusanci da mai cutar. Ga manyan hanyoyin watsa su: Na ɗaya, daga idan mutum mai cutar ya yi magana ko tari ko atishawa, sai su saki ɗigon numfashi da ke iya gangarowa a baki ko hancin mutanen da k... | audio/hau_m_571_he_spontaneous_033.flac | male | 30-45 | Tertiary | 97.96 | hausa | 40 | HE | |
HS1M2 | hau_m_HS1M2_ev_read_287 | Yau zan nazarci abubuwan da suka faru a rayuwata domin fahimtar darussan da ke ciki. | audio/hau_m_HS1M2_ev_read_287.flac | male | 15-29 | Secondary | 7.234 | hausa | 40 | EV | |
HM4F3 | hau_f_HM4F3_ev_read_083 | Wasu mutanen idan suna cikin damuwa, sai su sha taba sigari. | audio/hau_f_HM4F3_ev_read_083.flac | female | 60+ | Primary | 5.294 | hausa | 40 | EV | |
HT1F3 | hau_f_HT1F3_ev_read_081 | Kodayake jami'an tsaro suna aiki don a bi doka da oda, wasu suna kuma jawo tarzoma. | audio/hau_f_HT1F3_ev_read_081.flac | female | 15-29 | Tertiary | 8.654 | hausa | 40 | EV | |
HT1F1 | hau_f_HT1F1_ev_read_401 | Maryam za ta taimaki ƙanwarta don guje wa jarabar amfani da wayar hannu a kowane lokaci. | audio/hau_f_HT1F1_ev_read_401.flac | female | 15-29 | Tertiary | 7.114 | hausa | 40 | EV | |
HT1M3 | hau_m_HT1M3_ev_read_589 | Idan ta dawo daga aiki takan zo har gida, mu yi ‘yar hira | audio/hau_m_HT1M3_ev_read_589.flac | male | 15-29 | Tertiary | 4.714 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_634 | hau_f_634_ag_spontaneous_023 | Shin, kuna son kwakwa, kuna son kwakwa, kuna son dabino ko kuma kuna son kwakwar manja? To, ku biyo ni, domin yau za mi magana a kan iccen kwakwa tare da ziri’arsa. Iccen kwakwa de, wani ice ne daga ziri’ar “arasasiya family”, ana samun su ne da tsayi da girma. Ganyensu na da alamar fanka ko kamar gashin tsuntsu, ire-i... | audio/hau_f_634_ag_spontaneous_023.flac | female | 15-29 | Tertiary | 119.52 | hausa | 40 | AG | |
HT3M1 | hau_m_HT3M1_ev_read_377 | Ƙarancin cimaka kuwa yana iya haddasa kwashoko ga miliyoyin yara a ƙasashe duniya da ke cikin fatara. | audio/hau_m_HT3M1_ev_read_377.flac | male | 46-60 | Tertiary | 10.074 | hausa | 40 | EV | |
HS2F1 | hau_f_HS2F1_ev_read_578 | Fara makarantar sakandare na ba wa ɗalibai damar gano inda suka fi ƙwarewa. | audio/hau_f_HS2F1_ev_read_578.flac | female | 30-45 | Secondary | 6.794 | hausa | 40 | EV | |
HT1M2 | hau_m_HT1M2_ev_read_051 | Mutane da yawa suna dogara da ra’ayoyin kafafen sada zumunta wajen yanke shawara. | audio/hau_m_HT1M2_ev_read_051.flac | male | 15-29 | Tertiary | 7.334 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_421 | hau_m_421_ev_spontaneous_041 | barka da war haka a wannan fai-fai an mana bayani akan wato amfanin wato taimako da kuma bada wato kaman a ce goyon baya ko kuma bada wani agaji na hubbasa wanda zai taimake rayuwan wasu kaman yadda muka sani ne yadda ake dauko bayani ko da misali a gida ne ko kuma ince a gidaje akwai yara da suke tasowa wa'en da babu ... | audio/hau_m_421_ev_spontaneous_041.flac | male | 15-29 | Secondary | 179.7 | hausa | 40 | EV | |
HP3F1 | hau_f_HP3F1_ev_read_430 | A cikin taro, dole ne kowa ya samu damar magana. | audio/hau_f_HP3F1_ev_read_430.flac | female | 46-60 | Primary | 4.194 | hausa | 40 | EV | |
HAGT3M1 | hau_m_HAGT3M1_ev_spontaneous_007 | Idan aka bi al’ada yadda ya kamata, za a sami kyakkyawar rayuwa a sabon gidan da mace za ta shiga. | audio/hau_m_HAGT3M1_ev_spontaneous_007.flac | male | 46-59 | Tertiary | 9.394 | hausa | 40 | EV | |
HP1M3 | hau_m_HP1M3_ev_read_392 | Karɓar tallafi daga gwamnati a lokacin annoba ya na ragewa al'umma raɗaɗi. | audio/hau_m_HP1M3_ev_read_392.flac | male | 15-29 | Primary | 7.414 | hausa | 40 | EV | |
HT3M2 | hau_m_HT3M2_ev_read_163 | Muna yin shirin karatu da nishaɗi don kada ɗaya ya mamaye wani. | audio/hau_m_HT3M2_ev_read_163.flac | male | 46-60 | Tertiary | 8.054 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_180 | hau_m_180_ag_spontaneous_087 | baya ga manomi ya gama girbin sa yakan ɗauki masarar nan ya kaita wurin da zai adana ta kowanni manomi in ya noma abu mai yawa ya kamata ya samu wurin da zai iya adana wannan abun da ya shuka musamman ga manoma masara sukan zo su sanya ta ta bushe bayan sun saka ta ta bushe zasu zo su raba ta da kusonta domin su ɗura t... | audio/hau_m_180_ag_spontaneous_087.flac | male | 15-29 | Primary | 90.96 | hausa | 40 | AG | |
HP1F1 | hau_f_HP1F1_ev_read_205 | An gudanar da liyafar karrama dattijan gari a filin makarantar firamare. | audio/hau_f_HP1F1_ev_read_205.flac | female | 15-29 | Primary | 7.034 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_190 | hau_f_190_ag_spontaneous_016 | Ajiye amfanin gona don safarar su zuwa kasuwa mai nisa yana da matukar mahimmanci domin tabbatar da cewa kayan sun kasance cikin kyawawan hali har zuwa lokacin da za a siyar da su. Wannan yana taimakawa wajen kiyaye lafiyar amfanin gona da kuma rage asara ga yadda ake ajiye su domin zuwa kasuwa mai nisa. Farko za a sam... | audio/hau_f_190_ag_spontaneous_016.flac | female | 15-29 | Primary | 113.322667 | hausa | 40 | AG | |
HT2F1 | hau_f_HT2F1_ev_read_392 | Wasu lokutan kuma, idan abin baƙin ciki ya zo, ko akwai kuɗi ba za a samu farin ciki ba. | audio/hau_f_HT2F1_ev_read_392.flac | female | 30-45 | Tertiary | 7.974 | hausa | 40 | EV | |
HP1M2 | hau_m_HP1M2_ev_read_196 | Saminu yana matuƙar son kallon fim da kuma karatu sosai | audio/hau_m_HP1M2_ev_read_196.flac | male | 15-29 | Primary | 7.094 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_1279 | hau_f_1279_ev_spontaneous_009 | Barka da war haka, lokaci na karshe da naji daɗin wato, zama da iyali na, wannan lokacine, wato da yara, suka samu hutun makaranta a wannan lokaci naji daɗin sosai, gamida wato yanayin wurare na shaka tawa na wasanni na yara da muka fita dasu wato da me gidan baki ɗaya yayinda a wannan lokaci na hutu wato yara basa mak... | audio/hau_f_1279_ev_spontaneous_009.flac | female | 46-60 | Tertiary | 162.78 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_1538 | hau_m_1538_he_spontaneous_009 | Salama alaikum [?] Menene ciwon nonon mata? Ciwon nonon mata wanda a ke kira da breast cancer a turance, cuta ce da ke faruwa lokacin da koyoyin halitta na cikin nono su ka fara girma, ba bisa ga ida ba wadannan kwayoyi na cigaba da yaduwa su su kafa kunburi kuma idan ba'a kula ba da wuri, su na iya yaɗuwa zuwa wasu ts... | audio/hau_m_1538_he_spontaneous_009.flac | male | 46-60 | Tertiary | 224.94 | hausa | 40 | HE | |
HS3M2 | hau_m_HS3M2_ev_read_525 | Yin wasa tare da abokai yana ba ni damar sakewa da jin daɗin rayuwa. | audio/hau_m_HS3M2_ev_read_525.flac | male | 46-60 | Secondary | 9.374 | hausa | 40 | EV | |
HS3M2 | hau_m_HS3M2_ev_read_321 | Gasar rawa yayin bukukuwa suna nishaɗantarwa da samar da gasa mai kyan gani. | audio/hau_m_HS3M2_ev_read_321.flac | male | 46-60 | Secondary | 9.574 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_051 | hau_m_051_ev_spontaneous_024 | Wannan na magan tsarin dare me sanyi dan samun natsuwa da kwanciyan hankali, al’adun rayuwa cikin sauƙi da an dare me farin ciki bayan gajiyan yini, samun natsuwa da shirya kai dan dare me kyau yana da mahimmanci, ga wasu hanyoyi masu sauƙi da za ka iya aiwatarwa dan samun kwanciyan hankali da kuma hutun dare me daɗi. ... | audio/hau_m_051_ev_spontaneous_024.flac | male | 15-29 | Tertiary | 112.9 | hausa | 40 | EV | |
HT1M2 | hau_m_HT1M2_ev_read_521 | Fahimtar wariya yana taimakawa wajen gujewa ɗaukar mutane ba daidai ba. | audio/hau_m_HT1M2_ev_read_521.flac | male | 15-29 | Tertiary | 6.774 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_106 | hau_m_106_ev_spontaneous_008 | a wannan hoto ma zamu ga kasuwa ne wato ga mata nan a zaune ga yara duk dai a wannan kasuwa ga kayayyaki nan an fito dasu an karkasa ga nan muna ganin tumatir muna ganin a yaba muna ganin can dankalin hausawa nan ga wata mata nan ta zauna gaban kayanta tana tana taɗi tana jiran mai siya yazo ya siya ta siyar masa ta sa... | audio/hau_m_106_ev_spontaneous_008.flac | male | 15-29 | Tertiary | 93.24 | hausa | 40 | EV | |
HP1M2 | hau_m_HP1M2_ev_read_408 | Bayan gajiyar aiki, yana yin wanka da sabulu mai ƙamshi don jin daɗi. | audio/hau_m_HP1M2_ev_read_408.flac | male | 15-29 | Primary | 6.014 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_1120 | hau_f_1120_ag_spontaneous_007 | Wannan hoto yana nuna mana mutane ne guda biyu riƙe da jarkunan su na kamun kifi a bisa dukkan alama masunta ne, na gaban da na bayan dukkansu. Na gaban yana sanye da riga mai alaman ruwan rawaya da buhu a hannunshi sannan kuma ya rataye wannan abin da suke tarko suna kamun kifi, a bisa dukkan alamu waɗannan mutane mas... | audio/hau_f_1120_ag_spontaneous_007.flac | female | 30-45 | Tertiary | 162.06 | hausa | 40 | AG | |
HT3F1 | hau_f_HT3F1_ev_read_204 | A rediyo an ce kada kowa ya bi titin Gidan Zu, saboda ana zargin zakuna sun kwance a daren jiya | audio/hau_f_HT3F1_ev_read_204.flac | female | 46-60 | Tertiary | 8.854 | hausa | 40 | EV | |
HS1M2 | hau_m_HS1M2_ev_read_201 | Za a kai tufafi ga marayu a sansanin gudun hijira a Borno. | audio/hau_m_HS1M2_ev_read_201.flac | male | 15-29 | Secondary | 5.194 | hausa | 40 | EV | |
HM4F2 | hau_f_HM4F2_ev_read_326 | Yana da kyau a raba nauyin kulawa da iyali don rage wahala. | audio/hau_f_HM4F2_ev_read_326.flac | female | 60+ | Primary | 7.074 | hausa | 40 | EV | |
HP1F1 | hau_f_HP1F1_ev_read_273 | shirya bukukuwan gargajiya yana nuna girmamawa ga al’adu da tarihin al’umma. | audio/hau_f_HP1F1_ev_read_273.flac | female | 15-29 | Primary | 7.034 | hausa | 40 | EV | |
HT1M4 | hau_m_HT1M4_ev_read_488 | Zan haɗa kai da ƙungiyar tsaftace muhalli don inganta rayuwa. | audio/hau_m_HT1M4_ev_read_488.flac | male | 15-29 | Tertiary | 6.274 | hausa | 40 | EV | |
HS1M4 | hau_m_HS1M4_ev_read_292 | Tallafa wa matasa da shawarwari kan neman na-kai abu ne mai kyau. | audio/hau_m_HS1M4_ev_read_292.flac | male | 15-29 | Secondary | 6.454 | hausa | 40 | EV | |
HP1M3 | hau_m_HP1M3_ev_read_020 | Wasu mutane suna adana tsoffin kayan kakanninsu a gida don tunawa da su. | audio/hau_m_HP1M3_ev_read_020.flac | male | 15-29 | Primary | 5.814 | hausa | 40 | EV | |
HT1F1 | hau_f_HT1F1_ev_read_172 | Laraba za ta halarci biki a kudancin Najeriya don ganin bambancin al'adu. | audio/hau_f_HT1F1_ev_read_172.flac | female | 15-29 | Tertiary | 6.354 | hausa | 40 | EV | |
HS2F2 | hau_f_HS2F2_ev_read_584 | Karimatu ita ce babbar aminyar Shema’u, inda suke mutunta ra’ayoyin juna, saboda sun san suna da iyaka a rayuwar junansu | audio/hau_f_HS2F2_ev_read_584.flac | female | 30-45 | Secondary | 11.314 | hausa | 40 | EV | |
HT2M2 | hau_m_HT2M2_ev_read_396 | Na lura cewa tsara jadawalin ayyuka yana hana yawan ƙorafi tsakanin mazauna gida. | audio/hau_m_HT2M2_ev_read_396.flac | male | 30-45 | Tertiary | 7.554 | hausa | 40 | EV | |
HT3F2 | hau_f_HT3F2_ev_read_229 | Yau na yanke shawarar amfani da turaren da ke da ƙamshin 'ya'yan itace. | audio/hau_f_HT3F2_ev_read_229.flac | female | 46-60 | Tertiary | 6.274 | hausa | 40 | EV | |
HS1M4 | hau_m_HS1M4_ev_read_111 | Yawan kyauta yana ƙara danƙon soyayya tsakanin saurayi da budurwa. | audio/hau_m_HS1M4_ev_read_111.flac | male | 15-29 | Secondary | 5.974 | hausa | 40 | EV | |
HS2F1 | hau_f_HS2F1_ev_read_352 | Nazarin fannonin karatu a kan tsari ya na sauƙaƙa samun takardun shaida. | audio/hau_f_HS2F1_ev_read_352.flac | female | 30-45 | Secondary | 6.634 | hausa | 40 | EV | |
HS1M2 | hau_m_HS1M2_ev_read_048 | Ku daure ku dinga taimakon 'yanuwanku marasa ƙarfi kamar ku | audio/hau_m_HS1M2_ev_read_048.flac | male | 15-29 | Secondary | 6.034 | hausa | 40 | EV | |
HT1M3 | hau_m_HT1M3_ev_read_495 | Gaskiya tsafta ita ce rabin daɗin abinci a ko'ina ne ma. | audio/hau_m_HT1M3_ev_read_495.flac | male | 15-29 | Tertiary | 5.114 | hausa | 40 | EV | |
HS2F2 | hau_f_HS2F2_ev_read_406 | Kada ka damu, idan abokinka ya yi arziki sosai, kai kuma kana ta fama da rayuwa. | audio/hau_f_HS2F2_ev_read_406.flac | female | 30-45 | Secondary | 7.274 | hausa | 40 | EV | |
HM4F2 | hau_f_HM4F2_ev_read_435 | Ka siyo wa magena Lili kifi, don ta fi son sa | audio/hau_f_HM4F2_ev_read_435.flac | female | 60+ | Primary | 4.914 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_061 | hau_m_061_ag_spontaneous_008 | Wurin ganin an magance zaizayewar ƙasa akwai hanyoyi masu ɗan tarin yawa amma zan yi bayani kaɗan daga ciki waɗanda suka haɗa da ganin anyi shuke shuken bishiyoyi da kuma noma ayi noma akan ƙasashen da suke samun zaizayewar ƙasa ɗin da kuma wasu hanyoi kamar waɗanda suka shafi amfani da magudanan ruwa da kuma wasu tudu... | audio/hau_m_061_ag_spontaneous_008.flac | male | 15-29 | Tertiary | 151.32 | hausa | 40 | AG | |
HAGS1M1 | hau_m_HAGS1M1_ev_spontaneous_177 | Idan mutum yana so ya guji cin bashi, dole ne ya tanadi don lokutan matsala. | audio/hau_m_HAGS1M1_ev_spontaneous_177.flac | male | 15-29 | Secondary | 9.974 | hausa | 40 | EV | |
HT3M1 | hau_m_HT3M1_ev_read_409 | Ƙungiyoyin taimakon juna na unguwanni su ne ƙashin bayan gina al'umma. | audio/hau_m_HT3M1_ev_read_409.flac | male | 46-60 | Tertiary | 5.714 | hausa | 40 | EV | |
hau_f_600 | hau_f_600_ev_spontaneous_033 | Gareji kala kala ne. Akwai gareji na cikin gida da ake ajiye ajiyan mota ko abin hawa, akwai gareji na em em na gyara abubuwan hawa da sauran su akwai kuma gareji na ajiyar mota da ba a cikin gida yake ba, wannan an keɓe shi ne wuri na daban . Gareji in an buɗe gareji in dai na dan gyaran mota ne da kuma ajiyan kayan d... | audio/hau_f_600_ev_spontaneous_033.flac | female | 15-29 | Tertiary | 111.7 | hausa | 40 | EV | |
HS1M4 | hau_m_HS1M4_ev_read_177 | Bayan aure, Sadiya ta fahimci cewa ƙauna tsakanin ma’aurata tana ƙarfafa alaka a lokuta masu wahala. | audio/hau_m_HS1M4_ev_read_177.flac | male | 15-29 | Secondary | 8.454 | hausa | 40 | EV | |
HP1F1 | hau_f_HP1F1_ev_read_503 | ‘Yan sanda sun ceto yara sha huɗu daga wuraren daban-daban a Jihar Nasarawa. | audio/hau_f_HP1F1_ev_read_503.flac | female | 15-29 | Primary | 10.814 | hausa | 40 | EV | |
HP1M3 | hau_m_HP1M3_ev_read_318 | Yana da kyau mutum ya tanadi don hutu ko tafiya zuwa ƙasashen waje. | audio/hau_m_HP1M3_ev_read_318.flac | male | 15-29 | Primary | 7.334 | hausa | 40 | EV | |
HAGT1F3 | hau_f_HAGT1F3_ev_spontaneous_235 | A yau, zan ba kaina dama in huta idan na gaji da aiki. | audio/hau_f_HAGT1F3_ev_spontaneous_235.flac | female | 15-29 | Tertiary | 5.793 | hausa | 40 | EV | |
HS3F1 | hau_f_HS3F1_ev_read_497 | A wasu wurare, ɗaga hannu sama kadan na nufin gaisuwa ba tare da magana ba. | audio/hau_f_HS3F1_ev_read_497.flac | female | 46-60 | Secondary | 11.194 | hausa | 40 | EV | |
HT1F1 | hau_f_HT1F1_ev_read_035 | A wasu al’adu, an haramta shan giya gaba ɗaya, yayin da wasu ke kallonta a matsayin al’ada. | audio/hau_f_HT1F1_ev_read_035.flac | female | 15-29 | Tertiary | 7.534 | hausa | 40 | EV | |
hau_m_1020 | hau_m_1020_ag_spontaneous_035 | Lokacin da natashi yin girbi watakan na abunda na noma zan girbe na kasance cikin farin ciki mara misaltuwa da kuma tunanin cewa zan girbe abunda zan samu mai yawa wanda xan taimaki kaina da iyalina kuma in taimaki 'yan uwa da abokan arziki. Na kasance ina mai murna da kyautata zaton zan samu abu mai yawa wanda zan iya... | audio/hau_m_1020_ag_spontaneous_035.flac | male | 46-60 | Tertiary | 153.48 | hausa | 40 | AG | |
hau_f_398 | hau_f_398_ag_spontaneous_025 | Haɗa manja yanzun dai wata mata ce zaune akan abun zama ta sa atamfa a jikinta ga turmi a gabanta da niƙaƙƙen manja, an zuba mai ruwa kamar yadda na yi bayani a baya niƙaƙƙe bayan an silala wannan kwakwan manjan, bayan an ɗauko shi an sassako shi daga bishiya za a zo a zuba shi a tukunya a silala shi, bayan an silala s... | audio/hau_f_398_ag_spontaneous_025.flac | female | 15-29 | Tertiary | 112.6 | hausa | 40 | AG |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.